Isa ga babban shafi
Amurka

Biden ya bada umurnin ci gaba da binciken tarzomar Capitol da Trump ya dakatar

Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umurnin mika wasu takardu dake kunshe da bayanan da suka shafi tarzomar magoya bayan magabacinsa Donald Trump a majalisar dokokin kasar a ranar 6 ga watan Janairu ga kwanitin Majalisar dake gudanar da bincike akai.

Magoya bayan shugaban Amurka Donald Trump lokacin da suka mamaye majalisar Dokokin kasar na Capitol dai-dai lokacin da 'yan majalsiar ke zaman tabbatar da zabin Joe Biden a shugabancin Amurka ranar 6 ga watan Janarairun 2021.
Magoya bayan shugaban Amurka Donald Trump lokacin da suka mamaye majalisar Dokokin kasar na Capitol dai-dai lokacin da 'yan majalsiar ke zaman tabbatar da zabin Joe Biden a shugabancin Amurka ranar 6 ga watan Janarairun 2021. SAUL LOEB AFP
Talla

Zababbun jami'an da ke jagorantar wannan kwamiti sun yi barazanar gurfanar da wasu mukarraban  tsohon shugaba Donald Trump da suka ki ba da hadin kai da laifin raina Majalisa .

An kafa wannan "kwamiti na musamman" na Majalisar Wakilai don tantance rawar da Donald Trump ya taka a harin da magoya bayansa suka kai ginin majalisar dokokin kasar na Capitol, yayin da ake tabbatar da nasarar Joe Biden a zaben shugabancin Amurka.

Tsohon shugaban ya yi amfani da damar karfin ikon shugaban kasa wajen hana mika takaddun da suka danganci rikicin magoya bayansa a Capitol don kauce mika su ga kwamitin binciken.

To sai dai a ganin Joe Biden ta bakin kakakin Fadar White House Jen Psaki bai halasta ayi amfani da ikon shugaban kasa ba wajen hana mika bayanan ga kwamitin bincike.

Shugaban na ganin yana da matukar mahimmanci ga Majalisa da Amurkawa su gane komai dangane da abubuwan da suka faru a ranar 6 ga watan Janairun wannan shekara ta 2021, domin hana sake faruwar haka nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.