Isa ga babban shafi
Olympics - Kwallon Kafa

Trump ya caccaki tawagar kwallon matan Amurka duk da lashe Tagulla

Tawagar kwallon kafar Amurka ajin mata ta lashe lambar yabo ta Tagulla a gasar wasannin Olympics da ke gudana a Japan.

Kungiyar kwallon kafar matan Amurka yayin murnar samun nasarar doke takwarorinsu na Netherlands a gasar Olympics da ke gudana a Japan.
Kungiyar kwallon kafar matan Amurka yayin murnar samun nasarar doke takwarorinsu na Netherlands a gasar Olympics da ke gudana a Japan. © REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Sai dai tsohon shugaban Amurkan Donald Trump ya caccaki kungiyar wadda ya ce ta gaza lashe lambar yabo ta Zinare ce saboda karkatar da suka yi cikin harkokin siyasa.

A cewar Trump ba domin tsoma baki cikin siyasa ba, da kuma mutanen marasa nutsuwar da ke jagorantarsu ba, tawagar kwallon kafar za ta iya nuna bajintar da ta zarce wadda suka yi wajen samun Tagulla a gasar Olympics.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.