Isa ga babban shafi
Olympics

‘Yan wasan ninkayar Amurka sun yi karyar an ma su fashi a Brazil

Wasu ‘Yan wasan ninkayar Amurka da aka tsare a Brazil kar zargin cewar an yi mu su fashi sun bar kasar bayan sun amsa cewar karya suka yi. Hukumomin ‘Yan Sandan Brazil sun tsare ‘Yan wasan biyu inda suka gudanar da bincike wanda ya nuna cewar babu wanda ya mu su fashi.

'Yan wasan ninkayar Amurka Jack Conger and Gunnar Bentz sun fice Brazil bayan sun yi karyar an masu fashi
'Yan wasan ninkayar Amurka Jack Conger and Gunnar Bentz sun fice Brazil bayan sun yi karyar an masu fashi REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Shugaban hukumar wasan Olympics an Amurka Scott Blackmun ya nemi gafarar Brazil kan abin da ya faru.

Batun dai ya mamaye kanun labarai a wasannin Olympics na Rio bayan ‘Yan wasan ninkayar Amurka hudu sun ikirarin cewa an tare su da bindiga a wani gidan sayar da mai a Rio a ranar Lahadi.

Tuni kuma biyu daga cikinsu suka bar Brazil suka koma gida sakamakon bacin sunan da suka janyo wa Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.