Isa ga babban shafi
Amurka

Ku ajiye ban-bancin siyasa saboda Olympics- Obama

A yayin da aka shiga wasannin Olympics gadan-gadan a birnin Rio de Janeiro na Brazil, shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci daukacin kasarsa da su ajiye ban-bance ban-bancen siyasa a gefe don hada kai wajen mara wa Amurkawa da ke fafatawa a gasar ta Olympics.

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Shugaban ya bukaci haka ne a hirarsa da aka watsa ta kafar rediyo da intanet a yau  Asabar, inda ya jinjina wa tawagar kasarsa da ke Brazil.

Wannan dai na zuwa ne a da dai lokacin da kasar ke fama da cece-kucen siyasa da suka hada da kalaman nuna kyama ga Amurkawa musulmai musamman daga bangaren dan takaran shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Republiocan, Donald Trump.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.