Isa ga babban shafi
Brazil-MDD

Ministan Lafiyar Brazil ya kamu da covid-19 a taron MDD

Gwaji ya gano ministan lafiyan Brazil Marcelo Queiroga na dauke da cutar da covid-19 kwana guda bayan halartar bude taron babban zauren majalisar dinkin duniya da ya ke wakiltar shugaba Jair Bolsonaro.

Ministan Lafiya na Brazil Marcelo Queiroga tare da shugaban kasa Jair Bolsonaro yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amurka.
Ministan Lafiya na Brazil Marcelo Queiroga tare da shugaban kasa Jair Bolsonaro yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York na Amurka. EVARISTO SA AFP
Talla

Sanarwar da gwamnatin Brazil ta fitar ta ce ilahirin tawagar da ke tare da Queiroga an yi musu makamancin gwajin amma babu wanda ke dauke da cutar.

Ministn lafiyar wanda tun tuni ya karbi allurar rigakafin covid-19, shi ne jami’in tawagar Brazil na biyu da aka gano ya harbu da cutar bayan halartar taron na Majalisar dinkin duniya a birnin New York.

Bayanai sun ce Queiroga mai shekaru 55 zai ci gaba da killace kansa a Amurka har zuwa lokacin da zai warke daga cutar yayinda sauran tawagar Brazil za ta koma gida.

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro wanda har yanzu bai karbi tashi allurar rigakafin covid-19 din ba yana ya wo ne ba tare da kyallen rufe hanci da baki ba, yayinda ya ke ci gaba da nanata cewa shi ne dan Brazil na karshe da zai karbi rigakafin cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.