Isa ga babban shafi
GABAS-TA TSAKIYA

Kafa kasar Falasdinu zai warware rikicin Gabas ta Tsakiya - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewar kafa kasar Falasdinu akan hanyar diflomasiya ce kawai zai tabbatar da makomar zaman lafiyar Isra’ila a Yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka Joe Biden yana gabatar da jawabin sa na farko a Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Amurka Joe Biden yana gabatar da jawabin sa na farko a Majalisar Dinkin Duniya TIMOTHY A. CLARY POOL/AFP
Talla

Biden wanda yake jawabin sa na farko a taron Majalisar Dinkin Duniya a matsayin shugaban kasa, ya jaddada matsayin Amurka na tabbatar da tsaron Isra’ila a koda yaushe.

Shugaban yace yana da yakinin cewar samun kasashe biyu shine zai tabbatar da zaman lafiyar kasar Yahudawa ta isra’ila domin ci gaba da wanzuwar ta tare da kasar Falasdinu cikin ‘yancin dimokiradiya.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz Thaer GHANAIM, Menahem KAHANA PPO/AFP/File

Biden yace amma akwai duguwar tafiya kafin cimma wannan buti, duk da yake ba zasu yanke kauna ba wajen fatar ganin an samu ci gaba.

Wannan matsayi na shugaba Biden ya nuna sauyin matsayin Amurka bayan saukar shugaba Donald Trump daga karagar mulki wanda gwamnatin sa taki goyan bayan kafa kasar Falasdinu, abinda ya sa shugabannin Falasdinawa suka ki tattaunawa da wakilan ta domin warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

A kwanakin da suka gabata shugaba Biden ya karbi bakuncin Firaministan Isra'ila Naftali Bennet da kuma ministan tsaro Benny Gantz inda ya gana da su a lokuta daban daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.