Isa ga babban shafi
Isra'ila - Gaza

Jiragen saman yakin Isra'ila sunyi ruwan bama-bamai a Gaza

Rundunar sojin saman Isra’ila tace, jiragen samanta sunyi luguden wuta wasu wurare biyu a Gaza a wannan Lahadin, bayan da mayakan yankin suka yi arangama da sojoji a kan iyaka tare da harba balambalan masu fashewa zuwa kudancin Isra'ila.

Sojojin Isra'ila a kan iyakar Gaza.
Sojojin Isra'ila a kan iyakar Gaza. Menahem KAHANA AFP
Talla

Rikicin na baya-bayan nan ya zo ne yayin da Isra’ila da Masar ke ci gaba da sassauta takunkumi kan kasuwanci da tafiye -tafiye da aka sanya a Zirin Gaza, wanda kasashen biyu suka katse tun lokacin da kungiyar Islama ta Hamas ta kwace yankin Falasdinawa a shekarar 2007.

Sojojin Isra'ila sun ce "jiragen yakin sun kai hari kan sansanin sojan Hamas da ake amfani da shi wajen kera makamai da horo da kuma mashigin wani hanyar karkashin kasa da mayakan ke amfani da shi a kusa da Jabalia.

Sanarwar ta ce "Harin na mayar da martani ne ga kungiyar Hamas da ta harba balan-balan dauke wuta  a yankin Isra'ila da kuma tarzomar da ta auku kafin lokacin."

Sojojin sun ce duka abubuwan da suka faru “misalai ne na yadda Hamas ke ci gaba da amfani da dabarun ta’addanci da kai hari kan fararen hula.”

Babu wani rahoto daga Zirin Gaza na asarar rayuka sakamakon hare -haren na Isra'ila.

Da yake magana a Washington, inda ya gana da shugaban Amurka Joe Biden, Firayim Ministan Isra’ila Naftali Bennett ya ce ya dora wa Hamas da masu kishin Islama alhakin duk wani tashin hankali daga yankin Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.