Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Sauyin yanayi zai raba mutane sama da miliya 200 da muhallansu - Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi gargadin cewa, karancin albarkatun gona da rashin ruwa da kuma tumbatsar tekuna da sauran matsalolin sauyin yanayi, ka iya tilasta wa mutane miliyan 216 kaurace wa muhallansu nan da shekarar ta 2050.

Kwarin kogin Nile na kasar Masar na daga cikin yankunan da bankin duniya ta yi hasashen mutane za su kaurace wa saboda karancin ruwa.
Kwarin kogin Nile na kasar Masar na daga cikin yankunan da bankin duniya ta yi hasashen mutane za su kaurace wa saboda karancin ruwa. Khaled DESOUKI AFP/File
Talla

Bankin Duniyar mai cibiya a birnin Washington ya fitar da wani rahoto a shekarar ta 2018 da ke magana game da kaurar jama’a saboda tasirin sauyin yanayi a Kudancin  Asiya da Latin Amurka da kuma kasashen Afrika da ke kudu da Sahara,

A wancan rahoto, bankin ya yi hasashen cewa, mutane miliyan 143 za su iya kaurace wa muhallansu a wadannan yankuna na duniya  nan da shekarar ta 2050.

A sabon rahoton da ya fitar kuwa da ya kunshi sabbin yankuna uku da suka ha da da Gabashin Turai da Tsakiyar Asiya da Arewacin Afrika da kuma Gabashin Asiya har ma da yankin Pacific, bankin ya rubanya adadadin yawan mutanen da wannan matsala za ta shafe su nan da 2050.

Koda yake mataimakin shugaban bankin na duniyar bangaren samar da ci gaba, Juergen Voegele, ya ce, wannan adadi da suka yi hasashe ka iya sauyawa .

A cewarsa, muddin kasashen duniya suka fara rage gurbata muhalli da kuma maido da kyakkyawar alaka tsakanin halittu da muhalli, sannan kuma mutane suka sauya halayensu, to babu shakka za a samu raguwar kaurace wa muhalli da kashi 80 cikin 100 nan da shekarar ta 2050.

Ma’ana dai, adadin zai koma miliyan 44 a maimakon miliyan 216 da aka yi hasashen za su yi kaurar ta tilas saboda tasirin sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.