Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

An kaddamar da gidauniyar taimakawa Afghanistan

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya da su taimakawa kasar Afghanistan wajen ceto tattalin arzikin ta da kuma taimakawa mata tare da wadanda ‘yancin su ke fuskantar barazana.

Sakatare Janar Antonio Guterres
Sakatare Janar Antonio Guterres Javier Soriano AFP/Archivos
Talla

Yayin gabatar da jawabi wajen kaddamar da Gidauniyar Dala miliyan 606 domin taimakawa kasar domin ciyar da mutane akalla miliyan 11 da kuma kula da lafiyar kusan miliyan 3 da rabi, Guterres ya bayyana cewar mutanen Afghanistan sun fuskanci mummunar yanayin yaki na shekaru 20 da kuma matsalar tsaro tare da kuncin rayuwa.

Sakataren yace a bayyane take, wannan gidauniyar da aka kaddamar ba wai ta kunshi abinda za’a baiwa kasar ba ne, harma da bashin da kasar ke bin kasashen duniya.

Jawabin Antonio Guterres na zuwa ne kasa da wata guda bayan kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar, sakamakon rudanin da ya biyo bayan janyewar Amurka da kawayen ta.

Daga cikin Dala miliyan 606 da ake saran tarawa domin aikin jinkai a Afghanistan, akwai kudaden da za’a karkata wajen ciyar da jama’ar dake fama ad yunwa da kuma taimakawa marasa lafiya.

Sakataren yace Majalisar zata bada Dala miliyan 20 daga cikin asusun agajin gaggawan ta na Turai domin gudanar da aikin jinkai a Afghanistan, amma bukatar da ake da ita a kasar ta zarce abinda Majalisar ke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.