Talauci na iya dabaibaye kashi 97 cikin 100 na al’ummar Afghanistan - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Afghanistan na cikin hatsarin fukantar tabarbarewar al’amura, muddin kasashen duniya suka gaza daukar matakan samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga kasar.
Wallafawa ranar:
Majalisar ta ce ya zama dole a tabbatar kudade sun ci gaba da gudana cikin Afghanistan duk da cewar ba a san hakan ya zama taimako kai tsaye ga mayakan Taliban.
Sa’o’i bayan sake kwace iko da Taliban ta yi a Afghanistan karo na biyu, Amurka, da kasashen Turai da kuma manyan hukumomin Duniya suka katse baiwa kasar tallafi, da zummar dakile karfafa kungiyar ta Taliban.
A bayan bayan nan, Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ta fitar da wani rahoto da ya ce kimanin kashi 97 cikin 100 na al’ummar Afghanistan na iya fadawa cikin kangin talauci matukar ba a magance rikicin siyasa da tattalin arzikin kasar ba.
A halin yanzu kusan dala biliyan 10 na babban bankin Afghanistan da ke kasashen waje, hukumomin kasa da kasa suka kwace domin dakile kungiyar Taliban.
Sai dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Afghanistan Deborah Lyons ya shaida wa Kwamitin Tsaro a ranar Alhamis cewa ana bukatar samun hanyar shigar da kudi cikin kasar domin hana durkushewar tattalin arziki da tsarin zamantakewa lura da cewa kasar ta Afghanistan na fuskantar tarin matsaloli, ciki har da faduwar darajar kudin kasar, hauhawar farashin kayan abinci da man fetur da kuma karancin tsabar kudi a bankuna masu zaman kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu