Isa ga babban shafi
RIKICIN-AFGHANISTAN

Tsohon shugaban Afghanistan Ghani ya nemi gafarar jama'a

Tsohon shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya nemi gafarar jama’ar kasar akan yadda ya haure takalman sa ya gudu lokacin da mayakan Taliban suka mamaye wajen birnin Kabul.

Tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani
Tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani Jim Watson AFP/Archivos
Talla

Sanarwar da Ghani ya gabatarwa manema labarai tace yayi aiki da shawarar da jami’an tsaron fadar shugaban kasa ne suka gabatar masa na cewar gara ya fice domin kaucewa zubar da jini wanda ke iya kaiwa ga rasa dimbin rayuka.

Tsohon shugaban yace babu yadda dakarun Taliban zasu nufi fadar shugaban kasa ba tare da masu tsaron fadar sun mayar da martani ba, kuma hakan na iya haifar da kazamin fada.

Il y a plus de vingt ans, Sartaj Aziz, ministre des Affaires étrangères pakistanais recevait Mohammad Hassan Akhund à Islamabad, le 25 août 1999.
Il y a plus de vingt ans, Sartaj Aziz, ministre des Affaires étrangères pakistanais recevait Mohammad Hassan Akhund à Islamabad, le 25 août 1999. AFP - SAEED KHAN

 

Ghani ya kuma musanta cewar ya sace makudan kudade daga baitulmalin kasar lokacin da ya bar birnin Kabul, inda yace babu gaskiya cikin labarin.

Tsohon shugaban ya nemi jama’ar Afghanistan akan yadda kasar ta samu kan ta, wanda yace ba haka ya so ba, sai dai babu yadda ya iya.

Tuni dai kungiyar Taliban ta gabatar da sabbin shugabannin da zasu jagoranci kasar Afghanistan a karkashin jagorancin Mullah Mohammed Hassan Akhnud, wanda tsohon ministan ne a tsohuwar gwamnatin Taliban da tayi mulki a shekarun 1990 kafin gwamnatin Amurka ta kawar da ita daga mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.