Isa ga babban shafi
Muhalli - Amazon

Dajin Amazon yayi asarar murabba'in kilomita dubu 20 saboda sare bishiyoyi

Babban taron kiyaye muhalli mafi tasiri a duniya ya zartar da wasu kudurori a ranar Juma'a, cikinsu har da kira da a baiwa kashi 80 cikin 100 na Amazon daji mafi girma a duniya, da kashi 30 cikin 100 na doron kasa da teku kariya ta musamman, domin kawo karshen barazanar da nau’ikan halittu ke fuskanta na bacewa daga doron kasa.

Wani sashi na Amazon, daji mafi girma a duniya.
Wani sashi na Amazon, daji mafi girma a duniya. Douglas Magno AFP/File
Talla

Har yanzu dai, kungiyar da ke rajin kare muhalli da halittu ta duniya IUCN, wadda ke taro a birnin Marseille na Faransa, ba ta kai ga kafa wasu manufofi na kasa da kasa ba, sai dai shawarwarin da ta bayar a lokutan baya sun zama kashin bayan yarjejeniyoyin da kuma tarukan da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta kan kare Muhalli.

Wani sashi na bangaren dajin Amazon da ke cikin kasar Brazil.
Wani sashi na bangaren dajin Amazon da ke cikin kasar Brazil. AFP - JOAO LAET

Binciken masana ya nuna cewar cikin shekaru 20 da suka gabata, dajin Amazon ya yi asarar kusan murabba'in kilomita dubu 20 saboda sare bishiyoyi, yawancinsu ta hanyar kunna wutar sharar gona da gangan, wadda ke rikidewa zuwa gobarar daji.

Kwararrun sun yi gargadin cewa muddin dajin na Amazon ya ci gaba da fuskantar wannan matsala, babu makawa yanayinsa ka iya komawa irin na yankin Sahel, a maimakon yanki mai tarin bishiyoyi.

A baya bayan nan wata kungya da ke wakiltar ‘yan asalin nahiyar kudancin Amurka mai suna COICA, mai manbobi fiye da miliyan 2, suka bukaci ayyana kashi 4 cikin 5 na dajin Amazon a matsayin yanki mai kariya nan da shekarar 2025.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.