Isa ga babban shafi
IRAN-FARANSA

Ministan Iran yace Macron ya gayyace shi Paris domin tattaunawa

Sabon Ministan harkokin wajen Iran Amir-Abdollahian yace shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gayyace shi zuwa birnin Paris domin ganawa da shi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Yayin da yake tsokaci a kafar talabijin din Tehran bayan komawa gida daga taron tsaron da akayi a Bagadaza wanda Macron ya halarta, ministan yace Faransa na neman alaka ta kud-da-kud da kasar Iran.

Ministan yace sau biyu shugaba Macron ke zuwa wurin sa lokacin da taron ke gudana, inda yake shaida masa bukatar zuwa birnin Paris.

Abdollahian yace Macron daga bisani ya kira ministan harkokin wajen sa lokacin da suke tare, inda ya shaida masa cewar ya gayyace shi zuwa birnin Paris, saboda haka yana da kyau su sake bitar dangantakar dake tsakanin su da kuma ci gaba da tattaunawa.

Kasashen Faransa tare da Birtaniya da China da kuma Jamus na ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da Iran a shekarar 2015.

Yarjejeniyar ta yiwa Iran alkawarin taimaka mata wajen cirewa kasar takunkumin karya tattalin arziki domin ganin ita kuma ta daina shirin gina makamin nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.