Isa ga babban shafi
HADARIN-JIRGI

Akalla mutane 50 suka mutu a hadarin jirgin saman Philippines

Akalla mutane 50 suka mutu, yayin da wasu 50 suka jikkata lokacin da wani jirgin sojin Philippines dauke da sojoji ya fadi ya kuma kama da wuta bayan ya kaucewa hanyar saukar sa.

Inda jirgin sojin Philippines ya fadi
Inda jirgin sojin Philippines ya fadi Handout Joint Task Force-Sulu/AFP
Talla

Rahotanni sun ce akalla mutane 100 ke cikin jirgin kirar C-130 kuma akasarin su sabbin hafsoshin sojoji ne da suka sauke karatun su lokacin da jirgin ke kokarin sauka a tsibirin Jolo dake Yankin Sulu da rana.

Manjo Janar William Gonzales, kwamandan runduna ta musamman a Sulu ya ce an ga wasu sojojin suna tsalle suna ficewa daga jirgin kafin ya fadi a kasa inda ya kama da wuta.

Wannan ne hadarin jirgin soji mafi muni a tarihin kasar Philippines, yayin da Janar Gonzales ya bayyana yau a matsayin ranar bakin ciki a kasar.

Shugaban kasar Philippines Benigno Aquino l
Shugaban kasar Philippines Benigno Aquino l AP - Aaron Favila

Hafsan sojin ya bukaci jama’ar kasar da su yiwa sojojin da suka mutu da wadanda suka samu raunuka addu’a, yayin da ake ci gaba da neman sojoji 17 da suka bata.

Hotunan wurin hadarin da rundunar Sulu ta gabatar sun nuna yadda jirgin ya kone a tsakanin itatuwan kwakwa.

Masu aikin agaji bayan hadarin jirgin Philippines
Masu aikin agaji bayan hadarin jirgin Philippines via REUTERS - PHILIPPINES ARMY JFT SULU

Babban hafsan sojin Philippines Janar Cirillito Sobejana yace jirgin na dauke da sojoji ne daga Cayana de Oro dake kudancin tsibirin Mindanao lokacin da ya kasa gane wurin saukar sa a Jolo.

Kakakin rundunar sojin saman kasar Laftanar Kanar  Maynard Mariano yace zasu gudanar da bincike akan abinda yayi sanadiyar hadarin, yayin da kakakin sojin kasa Manjo Janar Edgard Arevalo yace ya zuwa yanzu sun dauki abinda ya faru ne a matsayin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.