Isa ga babban shafi
RIKICIN-FALASDINAWA

Falasdinawa sun yi zanga zangar adawa da shugaba Abbas

Daruruwan Falasdinawa yau sun gudanar da zanga zanga a Ramallah inda suka bukaci shugaban su Mahmud Abbas ya sauka daga mukamin sa saboda mutuwar wani mai fafutuka Nizar Banat wanda ya mutu a hannun sojojin Isra’ila wadanda suka tsare shi.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas AFP/File
Talla

Yan uwan Nizar sun shiga cikin jerin masu zanga zangar cikin su harda mahaifiyar sa wadda ke dauke da hotan marigayin wanda yayi kaurin suna wajen sukar shugabannin kungiyar Falasdinu, yayin da wasu kuma suke dauke da rubuce rubucen dake bukatar Abbas ya sauka daga shugabancin su.

Hassan Khreishah, tsohon shugaban majalisar dokokin Falasdinawa ya bayyana zanga zangar a matsayin goyan bayan Nizar Banat da kuma bukatar ganin an yi masa adalci.

Jami’an tsaron Falasdinawa sun tare hanyar dake zuwa ofishin Mahmud Abbas dake Ramallah domin hana masu zanga zangar isa wurin.

Falasdinawa na zanga zangar rusa musu gidaje a Silwan
Falasdinawa na zanga zangar rusa musu gidaje a Silwan REUTERS - AMMAR AWAD

A bangare guda kuma masu goyan bayan shugaba Abbas sun gudanar da ta su zanga zangar a birnin Hebron domin jaddada goyan bayan su a gare shi.

Mutuwar Banat ranar 24 ga watan Yuni ta haifar da zanga zangar kwanaki a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma suka daga kasashen duniya.

Banat mai shekaru 24 yayi rajistar tsayawa takarar zaben Yan Majalisun Falasdinawa a zaben da aka shirya gudanarwa a watan Mayu kafin shugaba Mahmud Abbas ya dakatar da shi.

Mahaifiyar Nizar Banat
Mahaifiyar Nizar Banat ABBAS MOMANI AFP

Binciken mutuwar sa da jami’an lafiya suka yi ya nuna cewar an lakada masa duka a kan sa da kirjin sa da wuyar sa da kuma hannuwa da kafafuwan sa kasa da awa guda bayan kama shi.

Iyalan sa sun ce ba zasu amince da sakamakon binciken da hukumomi zasu gabatar ba, saboda haka suna bukatar bincike na kasashen duniya.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Gabas ta Tsakiya Tor Wennesland ya bukaci hukunta masu hannu wajen kisan Banat, yayin da kungiyar kasashen Turai ta bukaci gudanar da bincike mai zaman kan sa.

Ita ma Amurka ta bayyana kaduwar ta da kisan inda ta bukaci gudanar da bincike akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.