Isa ga babban shafi
Falasdinawa - Isra'ila

'Yan sandan Isra'ila sun watsa taron Falasdinawa jim kadan bayan Sallar Juma'a

Rahotanni daga birnin Kudus sun ce ‘yan sandan Isra’ila sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa taron Falsdinawa bayan Sallar Juma’a, yayin da suke taron murnar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin mayakan su da Isra’ila.

Wasu 'yan sandan Isra'ila tsare da wasu Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa dake birnin Kudus.
Wasu 'yan sandan Isra'ila tsare da wasu Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa dake birnin Kudus. © Middle East Eye
Talla

Lamarin ya auku ne duk da soma aikin yarjejeniyar tsagaita wutar da Masar ta jagoranci kullawa, bayan shafe kwanaki 11 Isra’ila na kai hare-hare kan birnin Gaza, yayin da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harbawa Isra’ilar rokoki.

Falasdinawa akalla 243 cikinsu har da kananan yara 66 dakarun Isra’ila suka halaka yayin hare-haren da suka kaddamar ta sama da kasa kan birnin Gaza a tsawon kwanaki 11 da suka gabata.

A Isra'ila kuwa  makaman roka fiye da dubu 4 mayakan Hamas suka harba abinda yayi sanadin  mutuwar mutane 12 ciki har da yara 2, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.