Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Isra'ila ka iya nunawa Falasdinawa wariyar jinsi na tsawon lokaci - Faransa

Kasar Faransa ta bayyana fargabar samun matsalar nuna wariyar jinsi na dogon lokaci muddin Falasdinawa suka gaza wajen samun kasa ta kansu.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Jean Yves Le Drian ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai, inda yake cewa muddin aka gaza samarwa da Falasdinawa kasar su wadda zata wanzu daidai da Israila, tabbas za’a fuskanci matsalar nuna wariyar jinsi.

Ministan yace alamun samun wannan matsala na da girma muddin Israila ta cigaba da gudanar da harkokin ta a matsayin kasa daya tilo da kuma tabbatar da haka.

Le Drian yace yakin da aka kwashe kwanaki 11 ana fafata tsakanin Hamas da Israila ya bayyana muhimmancin farfado da shirin zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

Yayin da yake bayyana farin cikin sa da matakin da shugaban Amurka Joe Biden ya dauka na goyan bayan kafa kasar Falasdinu, ministan yace ya dace a dinga daukar matakan daya bayan daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.