Isa ga babban shafi
Iran

Al'ummar Iran na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

‘Yau al’ummar kasar Iran ke kada kuri’a a zaben shugaban kasar da hukumar da ke tantance ‘yan takara  ta bayyana a matsayin Zakaran Gwajin Dafi, la’akari da fafatawa mai zafi da za a yi tsakanin ‘yan takarar dake gwada farin jininsu.

Gangamin yakin neman zaben Ebrahim Raisi dake takarar shugabancin kasar Iran a birnin Teheran.
Gangamin yakin neman zaben Ebrahim Raisi dake takarar shugabancin kasar Iran a birnin Teheran. AFP - ATTA KENARE
Talla

Iraniyawa kusan miliyan 60 ne  ke kada kuri’a a wannan Juma’a inda za su zabi wanda zai gaji shugaba Hassan Rouhani, wanda ba zai sake takara ba, bayan da ya kammala wa’adi biyu na shekaru 4 kowanne.

Kafin zaben dai, al’ummar kasar sun yanke kauna da batun kada kuri’a, duba da yadda kasar ta fada cikin matsalar tattalin arziki, sakamakon takunkuman da Amurka ta kakaba mata, ga kuma tasirin annobar Korona.

Zaben na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ke cikin tattaunawa da manyan kasashen duniya da zummar ceto yarjejeniyar nukiliyarta, ta 2015, wanda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa daga ciki a 2018.

Dan takarar da ke kan gaba, wanda kafofin yada labaran kasar suka taba cewa shi zai gaji shugaban addinin kasar Ayatollahi Ruhollah Khamenei wanda zai cika shekaru 82 a watan Yuli shi ne Ebrahim Raisi.

‘Yan takara 600 ne aka tantance, aka rage su zuwa 7, kuma daya daga cikinsu ne mai ra’ayin kawo sauyi, kuma shine, tsohon shugaban babban bankin kasar, Abdolnasser Hemmati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.