Isa ga babban shafi
Iran - Nukilya

GCC ta bukaci tattauna batun makaman Iran masu linzami

Ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen yankin Tekun Fasha, a taron da suka gudanar a birnin Riyadh na Saudiyya, sun ce kamata ya yi a yi la’akari da shirin Iran na makamai masu linzami yayin tattaunawa kan batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a birnin Vienna.

Secretary-General of the Gulf Cooperation Council (GCC) Nayef Falah al-Hajraf and Saudi Arabia's Foreign Minister Prince Faisal bin Farhan Al Saud speak during a joint news conference at the Gulf Cooperation Council's (GCC) 41st Summit in Al-Ula, Saudi Arabia January 5, 2021. REUTERS/Ahmed Yosri
Secretary-General of the Gulf Cooperation Council (GCC) Nayef Falah al-Hajraf and Saudi Arabia's Foreign Minister Prince Faisal bin Farhan Al Saud speak during a joint news conference at the Gulf Cooperation Council's (GCC) 41st Summit in Al-Ula, Saudi Arabia January 5, 2021. REUTERS/Ahmed Yosri REUTERS - AHMED YOSRI
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wakilan  kasashen  Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Iran ke zaman lalubo mafita a game da yarjejeniyar  shirin nukiliyar  Iran ta shekarar 2015 a Vienna, a yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana aniyarsa ta maido da kasarsa cikinta, matsawar  Iran  za ta yi biyayya da abubuwan da aka zartas.

A sanarwar bayan taron da suka fitar, ministocin harkokin wajen kasashen na yankin Tekun Fasha  sun soki lamirin Iran a kan yadda take shiga da makamai Yemen don taimaka wa ‘yan tawayen Houthi, tare da yin Allah wadai da  harin ‘yan tawayen a kan lardin Magrib.

Bugu da kari, ministocin sun nuna rashin amincewarsu a game da duk  wani nau’in katsalandan a harkokin da ya shafi kasashen Larabawa, da ma dukkannin matakan da suka shafi damar mallakar ruwan Masa da Sudan.

Sun kuma yi tir da yawaitar safarar muggan kwayoyi daga Lebanon zuwa Saudiya bayan da hukumomin kasar suka haramta shigar da kayan marmari da sauran kayan gwari ta kasar da ke fama da tashin hankali, biyo bayan bankado dimbim kayayyakin sumogal a watan Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.