Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Kasashen duniya na tattaunawa da Iran kan nukiliyarta

A yau Talata bangarorin da suka amince da yarjejeniyar nukiliyar Iran ke komawa teburin tattaunawa a birnin Vienna domin farfado da yarjejeniyar bayan  sukurkucewarta.

Wakilan kasashe na tattaunawa da Iran a birnin Vienna.
Wakilan kasashe na tattaunawa da Iran a birnin Vienna. Handout APA/AFP
Talla

Tun a farkon wannan watan nan ne bangarorin da suka saura a cikin yarjejeniyar ta 2015 ke tattaunawa da juna da zummar maido da Amurka a cikin yarjejeniyar bayan janyewarta.

Wakilan kasashen Birtaniya da China da Faransa da Jamus da Iran da Rasha na zaman ganawa  karo na uku karkashin jagorancin Kungiyar Tarayyar Turai a wani kasaitaccen otel da ke birnin Vienna.

Kasar Iran ta ki  zaman cimma jituwa kai tsaye da Amurka, abin da ya sa wakilan Washington suka tare a wani otel na daban a birnin na Vienna, inda masu shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Turai ke kai musu rahoto kan halin da ake ciki.

A wani mataki na ramuwar gayya kan takunkuman da Amurka ta sake kakaba mata, Iran ta  kara kaimi wajen habbaka ayyukanta na  nukiliya tun shekarar 2019.

Iran ta ce, za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar ta nukilyar amma sai Amurka ta janye takunkuman.

Yanzu haka gwamnatin Joe Biden na son farfado da wannan yarjejeniya wadda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga cikinta.

Masu shiga tsakani na EU sun ce, ana samun ci gaba a zaman tattaunawar ta yau, amma dai akwai sauran aiki a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.