Martanin shugabannin duniya kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa
Shugabannin kasashe da na hukumomin kasa da kasa na cigaba da jan hankali kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa, inda wasu ke kiran da a kai zuciya nesa tare da taka tsan-tsan, wasu kuma na yin Alla-wadai da rikicin musamman da hare-haren jiragen yakin Isra'ila kan Falasdinawa a birnin Gaza da kuma makaman rokar da mayakan Hamas ke harbawa kan Isra'ilar.
Wallafawa ranar:
Zuwa yanzu dai kimanin mutane 75 suka rasa rayukansu ciki har da Falasdinawa 69 da 'yan Isra'ila 6 a rikicin dake barazanar rikidewa zuwa kazamin yaki.
Ita kuwa kungiyar tarayyar Turai EU A-wadai tayi da yadda Isra’ila ke korar Falasdinawa daga muhallansu, yayin da kuma ta ce ba za a lamunci hare-hare makaman rokar da Falasdinawa ke kaiwa fararen hula a Isra’ila ba, dan haka dole a kawo karshen rikicin.
Shugaban kungiyar hadin kan Larabawa ta Arab League Ahmed Gheit ya bayyana hare-haren jiragen yakin Isra’ila a matsayin tsantsar mugunta, tare da dorawa Isra’ilar alhakin barkewar rikicin na baya bayan nan, tare da kira ga hukumomin kasa da kasa su kawo karshen tashin hankalin.
Ita kuwa Turkiya cewa tayi ya dace gwamnatin Isra’ila ta gane cewar amfani da karfi ba zai murkushe ‘yancin neman hakkin Falasdinawa ba, yayin da shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci dukkanin bangarorin biyu su tagaita wuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu