Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Dakarun Isra'ila sun kashe Falasdinawa 21 yayin luguden wuta a Gaza

Falasdinawan akalla 21 sun rasa rayukansu sakamakon luguden wutar da jiragen yakin Isra’ila suka yi kan wasu yankunan zirin Gaza, bayan da Hamas ta harba rokoki zuwa cikin kasar ta Isra’ila.

Wasu Falasdinawa cikin jimamin mutuwar wani dan uwansu da ya rasa ransa sakamakon luguden wutar da Isra'ila ta yi kan yankunan Falasdinawa a zirin Gaza.
Wasu Falasdinawa cikin jimamin mutuwar wani dan uwansu da ya rasa ransa sakamakon luguden wutar da Isra'ila ta yi kan yankunan Falasdinawa a zirin Gaza. AP - Mohammed Ali
Talla

Lamarin dai na zuwa ne a yayin da ke rikicin da ake yi tsakanin falasdinawan da Isra’ila a Masallacin Al-Aqsa ke daukar sabon salo.

Cikin sanarwar da ta fitar a baya bayan nan, ma’aikatar lafiyar yankin Falasdinawa, cikin mutanen 21 da jiragen yakin Isra’ila suka kasha akwai kananan yara. Zalika rahotanni sun ce har zuwa wayewar garin yau talata jiragen yakin na Isra’ila sun kai wasu karin hare-haren kan Falasdinawan a zirin na Gaza.

Wani yankin zirin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa ruwan wuta.
Wani yankin zirin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa ruwan wuta. AP - Adel Hana

Farmakin Isra’ilar dai ya biyo bayan rokokin da mayakan kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta harba cikin kasar, bayan karewar wa’adin da ta dibarwa Isra’ila na neman ta janye jami’an tsaron daga Masallacin Al Aqsa, inda suka jikkata Falasdinawa akalla 300 a jiya Litinin kadai, biyo bayan afkawa Masallata da ‘yan sandan Isra’ila suka yi tare da harba barkonon tshuwa gami da bude musu wuta da harsasan roba, sa’o’I bayan rikicin karshen makon da ya kai ga jikkatar wasu Falasdinawan kusan 300 da kuma ‘yan sandan Isra’ila 20.

Tun a jiya Litinin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ya kunshi kasashe 15 yayi taro kan tashin hankalin da ake a birnin Kudus, sai dai har zuwa wannan lokaci bai fitar da sanarwar bayan taron ba, matakin da wasu jami’an Diflomasiyya suka ce hakan na da nasaba da matsayar Amurka kan cewar fitar da sanarwar ka iya munana halin rikicin Falasdinawa da Isra’ila, wadda kasashe da dama musamman na Larabawa da kuma Turkiya suka yi Allah-wadai da yadda take muzgunawa Falasdinawan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.