Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 69 yayin luguden wuta a Gaza

Rundunar sojin Isra’ila ta ce makaman roka akalla dubu 1 da 500 mayakan Falasdinawa suka harba cikin kasar a cigaba da fadan da suke gwabzawa biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu a birnin Kudusn a karshen makon da ya gabata.

Wani yankin na birnin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa luguden wuta.
Wani yankin na birnin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa luguden wuta. AP - Hatem Moussa
Talla

Rikicin tsakanin Isra’ila da Falasdinawa dai na cigaba da yin muni musamman a jiya Laraba, duka da kiraye-kirayen hukumomin kasa da kasa kan kawo karshensa.

A ranar Laraba dai hotunan bidiyon dake yawo a kafafe daban daban sun nuna yadda luguden wutar da jiragen yakin Isra’ila ke yi kan Falasdinawa a birnin Gaza yayi sanadin rushewar wani kafataren gini mai benaye da dama da ya kunshi ofisohin kafafen yada labarai.

Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa luguden wuta.
Wani yankin birnin Gaza da jiragen yakin Isra'ila suka yiwa luguden wuta. AP - Adel Hana

Kawo yanzu Falasdinawa akalla 69 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da yara 17, yayin da wasu sama da 300 suka jikkata.

Farmakin Isra’ilar dai ya biyo bayan makaman rokar da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas ke harbawa cikin kasar tun a ranar Litinin inda suka halaka mutane 6, bayan karewar wa’adin da Hamas din ta dibarwa Isra’ila kan janye jami’an tsaronta daga Masallacin Al Aqsa, inda suka ci zarafin fararen hula a yayin da suka ibada.

Tashin hankalin baya bayan nan dai ya samo asali ne kan tilasta korar wasu Falasdinawa daga wata unguwa mai suna Shiekh Jarrah, yankin da falasdinawa da Isra’ila suka dade suna shari’a kan hakkin mallakarsa tun shekarar 1972.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.