Isa ga babban shafi

Bai dace a samu cutar noma a doran kasa ba - MSF

Kungiyar Agaji da Medicins Sans Frotiers ta bayyana cewar lokaci yayi da za’a kawar da cutar noma wadda ke lalata sassan fuskar jama’a daga doran kasa.

Alamar kungiyar likitoci na kasa-da-kasa
Alamar kungiyar likitoci na kasa-da-kasa MSF
Talla

Kungiyar wadda ke hadin gwuiwa da kungiyar duniya dake yaki da cututtukan da akayi watsi da su a Yankin da ake fama da zafi, ta shirya wani taron masana da zai yi mahawara kan muhimmancin hada kai domin kawar da wannan cuta daga duniya.

Kungiyar tace abin takaci ne ganin yadda cutar noma kan hallaka mutanen da ta kama cikin makwanni 2 kacal muddin basu samu taimako wajen amfani da maganin yaki da cutar ba.

MSF tace wadanda suka tsira daga cutar kan rasa wasu sassan fuskar su dake basu wahala wajen cin abinci ko Magana ko gani ko kuma yin numfashi.

Kungiyar tace ana iya shawo kann abinda ke haddasa cutar da wuri ta hanyar amfani da magungunan dake kara garkuwar jiki, amma abin takaici shine yadda take cigaba da kasha mutane.

Froukje Pelsma, Daraktar dake kula da ofishin MSF a Najeriya tace duk da wadannan illolin da cutar keyi har yanzu Majalisar Dinkin Duniya bata baiwa cutar muhimmancin da ya dace ba.

MSF ta janyo masana daga sassan duniya domin fito da illar wannan cuta dan ganin an bata muhimmanci da kuma ware mata kudade na musamman dan ganin an kawar da ita.

Ita dai wannan cutar tafi kama yara ne dake kasa da shekaru 7 a yankunan da ake fama da talauci, kuma ta kan fara ne da kumbura dasoshi wanda akan iya shawo kan shi da maganin dake bunkasa garkuwar jiki.

Idan ba’a shawo kan cutar da wuri ba, cutar kan yadu cikin sauri wajen cinye naman fuska da kuma kasusuwa, abinda ke shafawa wadanda suka yi fama da cutar wani fenti na tsangwama.

Yanzu haka kungiyar MSF na aikin masu kula da wannan cuta a Jihar Sokoto dake Najeriya, kamar yadda Dr Bukola Oluyide, mataimakin Daraktan kungiyar a Najeriya ya tabbatar.

Tun daga shekarar 2014 MSF ke taimakawa asibitin Sokoto dake kula da cutar ta wani hadin gwuiwa da ma’aikatar lafiyar Najeriya, kuma tsakanin watan Agustar shekarar 2015 zuwa Octoban shekarar 2020 an yiwa masu fama da cutar 550 aiki domin gyara fuskokin su har sau 550.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.