Isa ga babban shafi
Duniya-Coronavirus

An gano wata mata mai dauke sabon nau’in cutar Korona a Colombia

Hukumomin Colombia sun bayana gano sabon nauyin kwayar cutar Corona da aka gano a Brazil ,jami’an kiwon lafiya sun gano cutar ne daf da kan iyaka da Brazil.

Misalin kwayar cutar coronavirus da na'urar Komfuta ta fitar.
Misalin kwayar cutar coronavirus da na'urar Komfuta ta fitar. NEXU Science Communication/via REUTERS
Talla

Karo na farko da hukumomin kiwon lafiyar Colombia suka tabbatar da haka a yakin daf da kan iyaka da kasar Brazil bayan bulluwar cutar ta covid 19.

Wata mata ce mai shekaru 24 aka gano cewa ta na dauke da kwayar cutar ,aka kuma gano cewa ta fito ne daga dayan biranen da aka gano sabon nau’in cutar,birnin Tabatinga dake tsakiyar kasar ta Brazil. A farkon watan janairun shekarar 2021 ,dubban ‘yan Brazil sun kaddamar da zanga-zangar adawa da gwamnati inda suke neman shugaban kasar Jair Bolsonaro yayi murabus, saboda gazawa wajen dakile yaduwar annobar Korona da ta halaka ‘yan kasar sama da dubu 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.