Isa ga babban shafi
Ghana

'Yan majalisa 15 sun kamu da cutar Korona a Ghana

Majalisar dokokin kasar Ghana ta takaita zamanta zuwa sau biyu a mako, bayan da manbobinta 15 suka kamu da cutar Korona.

Zauren majalisar dokokin kasar Ghana
Zauren majalisar dokokin kasar Ghana Modern Ghana
Talla

Yayin sanar da matakin kakakin majalisar ta Ghana Alban Bagbin yace dukkanin ‘yan majalisun sun mika kansu ne don gwajin cutar, kuma a halin yanzu suna killace har zuwa lokacin da za su murmure.

Kakakin ya ce akwai kuma karin wasu ma’aikatan majalisar dokokin 56 da suka kamu da cutar ta Korona, dan haka domin dakile yaduwar annobar suka takaita zama zuwa sau biyu a mako, a ranakun Talata da Alhamis.

A ranar Lahadin da ta gabata shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sake kafa dokar haramta tarukan jama’a, bayan hauhawar adadin masu kamuwa da cutar Korona, wadda ta sake barkewa zango na biyu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.