Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

Tilas kowa ya amfana da rigakafin annobar Coronavirus - WHO

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebereyesus ya jinjinawa kwararru kan namijin kokarin da suka yin a samar da alluran rigakafin cutar coronavirus, sai dai ya nanata cewar ya zama dole kowace kasa a duniya ta amfana da maganin.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS
Talla

Tedros ya bayyana haka ne a jiya Juma’a, bayan kammala jagorantar wani taron bitar halin da ake ciki kan yaki da annobar ta coronavirus a duniya, inda ya bukaci aiwatar da tsare-tsaren gaggauwa don wadata kowa da alluran rigakafin cutar.

A ranar litinin kamfanonin hada magunguna na Pfizer da BioNTech suka sanar da cewa alluran rigakafin da suke gwaji ya kai matakin kashi 90 na bada rigakafin kamuwa da annobar Covid-19, bayan gudanar da gwaje-gwajen da ya kunshi sama da mutane dubu 40, kasa da shekara guda bayan barkewar annobar daga China.

Sabbin alkaluman hukumomin lafiya dai sun nuna cewar yanzu haka annobar ta coronavirus ta halaka kusan mutane miliyan 1 da dubu 300 a sassan duniya, daga cikin sama da miliyan 52 da dubu 700 da suka kamu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.