Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

Shugaban WHO ya killace kansa saboda fargabar yada Korona

Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya ce ya killace kansa a daren Lahadi sakamakon cudanyar da ya yi da wasu mutane da daga bisani gwaji ya tabbatar suna dauke da cutar Coronavirus, amma ya jaddada cewa ba ya jin alamun cutar a jikinsa.

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS
Talla

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafin sadarwarsa na Twitter.

Tedros ya kasance a sahun gaba a kokarin da hukumar lafiya ta Majalisar dinkin duniya ke yi na dakile wannan cutar ta Covid 19.

Covid-19 ta lakume rayukan mutane kusan miliyan 1 da dubu dari 2, kuma ta kama sama da miliyan 46 a fadin duniya tun da ta bulla a China a karshen shekarar 2019.

Shugaban na hukumar lafiya ta duniya ya jaddada cewa yana da matukar mahimmanci al’umma su kiyaye ka’adojin kariya daga wannan shu’umar cuta.

Tsohon ministan lafiya da harkokin waje na kasar Ethiopia mai shekaru 55, ya shafe watanni 4 yana nanata cewa kowane mutum yana da mahimmiyar rawar da zai taka wajen dakile yaduwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.