Isa ga babban shafi

Yaki da korona na haifar da cikas ga kokarin kawar da TB -WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, annobar korona da yanzu haka ke addabar duniya na barazanar maida hannu agogo baya wajen kokarin yakin da ake yi don kawar da cutar tarin fuka.

Wani kenan da akewa allurar rigakafin cutar TB a Afirka ta Kudu
Wani kenan da akewa allurar rigakafin cutar TB a Afirka ta Kudu RODGER BOSCH / AFP
Talla

Rahoton na Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO na cewa, ana kiyasin tarin fuka kan iya janyo mutuwar karin mutane dubu 200 zuwa dubu 400 kafin karshen wannan shekarar ta 2020, kari kan fiye da miliyon 1 da dubu 400 a shekarar da ta gabata.

Kasashen da tarin fuka ya fi shafa irinsu India da Afrika ta kudu, na kokarin yaki da cutar, to sai dai ya rikide zuwa na annobar covid – 19.

Shugaban hukumar lafiya Tedros Adhanom Gebreyesu, yace Annobar covid -19 na barazanar shafe nasarar da aka samu a shekarun baya dangane da yaki da cutar tarin fuka.

A farkon watan Mayu, reshen yaki da cutar tarin fuka na Hukumar Lafiya ta Duniya yayi kiyasin cewa rufe birane da akayi na tsawon watani 3, saboda korona, kan iya samar da sabbin masu kamuwa da cutar TB har miliyo 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.