Isa ga babban shafi
Trump-Biden

Trump ya nanata zargin tafka magudi yayinda Biden ke gab da nasara

Yayin da dan takarar Jam’iyyar Democrat a zaben shugabancin Amurka Joe Biden ya kama hanyar lashe zaben shugaban kasar da aka yi, shugaba mai ci Donald Trump ya yi zargin magudi inda ya bukaci lauyoyin sa su ruga kotu, saboda zargin da ya yi na tafka magudi ganin yadda Biden ke samun kuri’u ta inda ba a tsamani.

Zuwa yanzu dai Biden na da kujerun wakilai 264 cikin 270 da kowanne dan takara ke bukata gabanin cancantar zama shugaban kasa a Amurka.
Zuwa yanzu dai Biden na da kujerun wakilai 264 cikin 270 da kowanne dan takara ke bukata gabanin cancantar zama shugaban kasa a Amurka. AFP
Talla

Samun gagarumar nasarar da Joe Biden ya yi a Jihohin Wisconsin da Michigan sun sa dan takarar ya yiwa shugaba Donald Trump fintinkau wajen samun kujerun wakilai 264 sabanin na shugaba Trump 214, yayin da ake dakon kuri’un Jihohin Georgia da Pennsylnavia inda ake saran ya samu cikon kujerun da zai zama shugaban kasa.

A bangare daya kuma shugaba Donald Trump na cigaba da zargin tafka magudi, ganin yadda jihohin da ake saran ya samu suka subuce masa zuwa wurin Biden.

Masu sanya ido kan zaben kasar sun ce da zaran an sanar da sakamakon Jihar Arizona wanda ake saran Biden ya lashe zai bashi nasarar da ya ke bukata wajen mayar da Trump shugaba mai wa’adi guda.

Rahotanni sun ce an fara gudanar da zanga zanga a wasu birane cikin su harda Portland inda aka girke daruruwan 'yan Sanda bayan da magoya bayan Trump suka kai hari kan shagunan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.