Isa ga babban shafi
Amurka

Biden ya kama hanyar lashe zaben Amurka

Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben Amurka, inda dan takarar Jam’iyyar Democrat Joe Biden ya sha gaban shugaba Donald Trump wajen samun yawon kuri’u.

Joe Biden da mataimakiyarsa  Kamala Harris
Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris AP Photo/Andrew Harnik
Talla

Sakamakon zaben na Amurka na ci gaba da shigowa kuma alkaluma sun nuna cewa, Joe Biden na Jam’iyyar Democrat ya lashe jihohi masu muhimmanci da suka hada da California da New York har ma da babban birnin kasar, wato Washington.

Shugaba Donald Trump kuwa ya samu nasara a jihohi irinsu Kentucky da Missouri da Oklahoma da Tennessee da Ohio, kuma da ma ya lashe wadannan jihohi a shekarar 2016.

Sakamakon ya nuna cewa, Biden na da kashi 49.8 na yawan kuri’un da aka fitar kawo yanzu, yayin da Trump ke da kashi 48.61.

Ma’ana dai Biden ya samu kuri’u miliyan 60 da dubu 537 da 520, inda shi kuma Trump ya samu kuri’u miliyan 59 da dubu 289 da 433.

Kazalika Biden ya fi samun yawan kuri’un Wakilan Kwamitin Zaben Shugaban Kasa da ake kira Electoral College, inda yake da 223, sabanin Trump da ya samu 145.

Wannan Kwamiti na Electoral College shi ke da alhakin karshe na tantance wanda zai zama shugaban kasa, kuma da zaran dan takara ya samu kuri’u 270 na kwamitin, to kai tsaye za a yi masa barka da samun nasara.

Trump ya yi zargin satar kuri'a, yayin da Biden ke cewa, yana kan hanyar samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.