Isa ga babban shafi
Amurka

Democrats ta kare rinjayenta a majalisar wakilan Amurka

Jam’iyyar Democrats ta cigaba da kare rinjayen da take da shi a zauren majalisar wakilan Amurka kamar yadda masu sharhi suka zata.

Kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi
Kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Kafofin yada labaran Amurka sun ruwaito cewar, Democrats ta kuma kara adadin ‘yan majalisarta a zauren majalisar wakilan mai kujeru 435.

Kafin gudanar zabukan Amurkan kafofin yada labaran Amurka da suka hada da Fox News da NBC News sun yi hasashen kakakin majalisar wakilan kasar Nancy Pelosi ta Democrats za ta kara samun rinjaye da karin kujeru 4 zuwa 5.

Nasarar za ta baiwa Pelosi damar cimma aniyar soke kudurorin shugaba Donald Trump da dama, wadanda ya bada umarnin aiwatar dasu a zangonsa na farko, idan shugaban ya sha kaye kamar yadda ta sha alwashi a baya.

Daga cikin fitattun ‘yan majalisar na jam’iyyar Democrats da suka samu nasarar komawa zauren majalisar wakilan akwai matan nan hudu da suka fi sa shugaba Trump gaba a zangonsa na farko.

‘Yan majalisar kuwa sun hada da Alexandria Ocasio-Cortez, Ilhan Oumar, Rashida Tlaib da kuma Ayanna Pressley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.