Isa ga babban shafi
Amurka

Yadda manufofin Trump da Biden suka banbanta

'Yan takaran shugabancin Amurka wato shugaba Donald Trump da Joe Biden sun sha ban-ban a manufofinsu a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da kiwon lafiya hulda da kasashen ketare.

Joe Biden da Donald Trump.
Joe Biden da Donald Trump. Studio Graphique FMM
Talla

Annobar coronavirus na cikin manyan abubuwan da suka dauki hankali a zaben Amurka na wannan lokaci. Shugaba Donald Trump ya kafa kwamiti a karshen watan Janairu, yana mai cewa, a yanzu kwamitin ya mayar da hankalinsa kan kare lafiyar al’umma da kuma sake bude kasar.

Kazalika shugaban ya bada umarnin ware Dala biliyan 10 domin gaggauta samar da riga-kafin cutar.

Shi kuwa Jor Biden na son samar da wani shirin bibiyar masu dauke corona a fadin kasar, inda ya ce, zai kafa cibiyoyin gwajin cutar akalla 10 a kowacce jiha , sannan kuma gwajin zai kasance kyauta ga kowa, yayin da yake goyon bayan sanya takunkumi a daukacin kasar.

A bangaren sauyin yanayi kuwa, shugaba Trump dai na tantama, lamarin da ya sa ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar sauyin yanayi da kasashen duniya suka cimma a birnin Paris.

Shi kuwa Biden ya lashi takobin mayar da Amurka cikin wannan yarjejeniya da zaran ya lashe zaben shugabancin kasar. Sannan ya bayyana kudirinsa na ganin kasar ta daina fitar da hayaki mai gurbata muhalli baki daya nan da shekarar 2050.

Batun tattalin arziki na da muhimmanci a zaben Amurka, abin da ya sa Trump ya yi alkawarin samar da guraben ayyuka miliyan 10 cikin watanni 10, baya ga samar da sabbin kananan sana’o’I miliyan 1 a cewarsa.

Shugaban na kuma son rage kudin haraji domin karfafa wa kamfanoni guiwa don ganin sun ci gaba da kula da ma’aikata.

Shi kuwa Biden ya sanar da aniyarsa ta kara haraji amma ga masu karfi domin samun kudin gina kayayyakin more rayuwa ga talakawa.

Kazalika Mr. Biden na goyon bayan kara mafi karancin albashin ma’aika a matakin gwamnatin tarayya daga Dala 7 zuwa Dala 15 a kowanne sa’a guda.

Sai kuma bangare kiwon lafiya, inda shugaba Trump ya soke dokar inshorar lafiya ta tsohon shugaba Barack Obama, yana mai cewa, zai maye gurbinta da tsari mafi inganci, amma har yanzu babu wani bayani.

Shugaban ya kuma ce, zai rage farashin magunguna ta hanyar bada izinin shigo da magunguna masu rahusa daga kasashen ketare.

Shi kuwa Biden na son ci gaba da aiki da dokar inshorar lafiyar ta Obama tare da fadada ta da kuma kara yawan jama’ar da ke cin gajiyarta.

A game da manufofin ketare kuwa, shugaba Trump ya nanata kudirinsa na zabtare yawan dakarun Amurka da ke jibge a kasashen waje, sannan zai ci gaba da zuba jari a aikin soja a cewarsa.

Sai dai Biden a nasa bangaren ya yi alkawarin sabonta danganta da aminan Amurka.

Batun ‘yan sanda ya jima yana tayar da kura a Amurka musamman ganin yadda ake zargin su da kashe bakaken fata saboda kiyayya, amma Trump ya ce, ba ya tunanin bangaren ‘yan sanda na fama da matsalar nuna wariya, yayin da Biden ke cewa, tabbas akwai wannan matsala ta kyamar bakake a aikin na ‘yan sanda, kuma tuni ya samar da tsare-tsaren magance matsalar a cewarsa.

Sai kuma batun mallakar bindiga, inda shugaba Trump ya gabatar da kudirin tsaurara matakan mallamar makamin biyo bayan jerin hare-haren da aka kai a bara, sai dai har yanzu, shiru kake ji, malam ya ci shirwa.

Shi kuwa Mr. Biden ya gabtar da kudirinsa na haramta mallakar muggan makamai tare da takaita yawan bindigar da mutun zai iya mallaka a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.