Isa ga babban shafi
Twitter

Twitter ta soki wasu sakonnin Trump da ta ce suna neman tayar da hankali

Kamfanin sadarwa na twitter ya bayyana sakonni guda biyu da shugaba Donald Trump ya aike a matsayin marasa gaskiya da ke neman haifar da matsala a zaben shugaban kasar da ake dakon sakamako yanzu haka.

Kamfanin na Twitter ya bayyana sakonnin na Trump a matsayin wadanda za su iya tayar da hankulan jama'a dai dai lokacin da al'umma ke dakon sakamakon zabe.
Kamfanin na Twitter ya bayyana sakonnin na Trump a matsayin wadanda za su iya tayar da hankulan jama'a dai dai lokacin da al'umma ke dakon sakamakon zabe. OLIVIER DOULIERY / AFP
Talla

Shugaba Trump ya yi zargin cewar ana kawo wasu kuri’u da bai san inda su ke fitowa ba a Jihohin da ya ke samun rinjaye a gaban Joe Biden, abinda ya sa kamfanin ya rufe sakon na sa.

Mai Magana da yawun kamfanin ya ce sun dauki matakin yin haka ne saboda kare martabar su a idan jama’a da kuma hana mutane mahawara akan zargin.

Kafin dai wannan kamfanin ya dauki irin wannan matakin kan zargin da Trump ya yi cewar Jam’iyyar Democrat na kokarin sace zaben.

Kamfanin twitter ya ce ya dauki irin wannan mataki akan wasu sakonni da dama cikin su har da wadanda ke bayyana sakamako da ikirarin lashe zaben wadanda ba na hukuma ba ne daga dan takaran Sanata a Jihar North Carolina da kuma bayyana nasarar Biden a Winconsin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.