Mata hudu dake hana Trump sakat a Majalisa sun lashe kujerun su
Fitattun 'Yan Majalisun wakilai mata guda 4 dake adawa da manufofin shugaba Donald Trump a Amurka sun sake lashe kujerun su duk da adawar da shugaban ya dinga musu wajen ganin basu samu nasara ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
'Yan Majalisun sun hada da Alexandria Ocasio-Cortez da Ilhan Omar da Rashiad Tlaib da Ayyan Pressley.
Ocasio Cortez ta lashe kujerar ta dake Jihar New York cikin sauki, yayin da kafofin yada labaran Amurka suka sanar da cewar Ilhan Omar ta samu nasara a Minnesota, kamar yadda Ayanna Pressley ta samu a Massachussets da kuma Rashida Tlaib a Michigan.
Ilhan Omar ya bayyana farin cikin ta da sake dawowar kawayen ta a Majalisar wadanda ke takun saka da shugaba Donald Trump.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu