Isa ga babban shafi
Yemen

Yemen da 'yan tawayen Houthi sun yi musayar Fursinoni dubu 1

Bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen Houthi a Yemen sun fara musayar fursunoni tsakaninsu a wani yunkuri na kawo karshen yakin kasar da ke cikinn shekara ta 6 da farawa.

Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi na Yemen.
Wasu mayakan 'yan tawayen Houthi na Yemen. MOHAMMED HUWAIS / AFP
Talla

Bangaren gwamnatin da na ‘yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran sun amince da sakin fursinoni dubu 1 da 81 tsakaninsu karkashin yarjejeniyar da suka kulla yayin tattaunawarsu a Switzerland cikin watan jiya, adadin da ke matsayin mafi yawa na Fursunonin da suka saki tun bayan barkewar yakin a 2014.

Matakin sakin fursunonin bisa sa idon kungiyar agaji ta Red Cross wani bangare ne na yunkuri kawo karshen yakin wanda ke ci gaba da kassara kasar, baya ga jefa tarin jama’a cikin matsananciyar yunwa.

Yayin bikin dawowar fursunonin ‘yan tawayen na Houthi da aka kwaso cikin jirage 3 zuwa Sanaa Seiyum da kuma Saudi karkashin jagorancin Red Cross, bayan isarsu birnin Sanaa da ke hannun ‘yan tawaye, fursunonin wadanda suka gwabza yaki da Sojin gwamnatin Yemen da na hadakar kasashen larabawa bisa jagorancin saudiya sun samu kyakkyawar tarba daga jagororinsu inda suka rika dagaa hannu suna rera wake mai taken mutuwa ga Amurka mutuwa ga Isra’ila.

Kungiyar ta Red Cross ta bayyana matakin fara musayar fursunonin a matsayin babban ci gaba a yunkurin da ake na kawo karshen yakin kasar ta Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.