Jirgin yakin Saudiya ya yi hatsari a Yemen
Wani jirgin yaki mallakin rundunar hadakar da Saudiya ke jagoranta a Yemen, ya yi hatsari a arewacin lardin al-Jawf.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun rundunar hadakar da ke yaki da ‘yan tawayen Houthi na Yemen, ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin a daidai lokacin da yake kan gudanar da aiknsa.
Saudiya ba ta yi bayani ba game da rasa rai ko kumma jikkata a wannan hatsarin jirgin da i mayakan Houthi suka ce, su suka kakkabo shi.
A bangare guda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, fararen hula 31 aka kashe a wani harin sama da Saudiya ta kaddamar a jiya Asabar a lardin al-Jawf.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu