Isa ga babban shafi
MDD-Yemen

Kusan mutum milyan 10 na fama da matsananciyar yunwa a Yemen-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane milyan 10 ne ke fama da matsananciyar yunwa a kasar Yemen, tare da yin kira don ganin an taimaka wa wadannan mutane a cikin gaggawa.

Wani asibitin kula da yara a birnin Hodeida na Yemen.
Wani asibitin kula da yara a birnin Hodeida na Yemen. ESSA AHMED / AFP
Talla

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniyar WFP, ta ce tana bukatar akalla dalar Amurka milyan 737 kafin karshen wannan shekara domin sayen abincin da za ta raba wa mutanen da ke fama da yunwa a wannan kasa da yaki ya wargaza.

Mai magana da yawun hukumar ta WFP Elisabeth Byrs, ta bayyana wa mahalarta taron da hukumar ta gudanar a yau juma’a ta hoton bidiyo cewa, akwai bukatar kasashen duniya su samar da wadannan kudade a cikin gaggawa, lura da yadda matsalar ke ci gaba da ta’azzara.

Elysabeth ta ce kusan a kowace rana ana samun wadanda ke rasa rayukansu sakamakon yunwa a kasar ta Yemen, yayin da ake fuskantar hauhawar farashin kayayykin abinci a kasuwanni saboda karancinsa.

Wasu alkaluma da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya, sun nuna cewa kusan mutane milyan 20 ne ke fama da karancin abinci a kasar ta Yemen, yayin da milyan 13 daga cikinsu suka dogara da kungiyoyin agaji domin rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.