Isa ga babban shafi
Coronavirus

Jerin shugabannin kasashen Duniya da Coronavirus ta harba

Shugaban Amurka Donald Trump ya bi sahun sauran shugabannin duniya da suka kamu da cutar korona, bayan ya sanar da cewar shi da uwargidan sa sun kamu da cutar.

Kusan shugabannin Duniya 10 suka kamu da cutar ta Coronavirus tun bayan barkewarta cikin watan Disamban bara a yankin Wuhan na tsakiyar China.
Kusan shugabannin Duniya 10 suka kamu da cutar ta Coronavirus tun bayan barkewarta cikin watan Disamban bara a yankin Wuhan na tsakiyar China. AFP/Pool/Bernd von Jutrczenka
Talla

Trump wanda a farko bai yarda da bullar cutar ba, duk da yadda take hallaka rayukan jama’a, ko muhawararsu da abokin takarar sa Joe Biden, shugaban ya yi wa Biden shagube kan yadda ya ke sanya kyallen rufa baki da hanci a koda yaushe.

Kafin yanzu, Firaministan Birtaniya Boris Johnson shi ne shugaba na farko da ya kamu da cutar a watan Afrilu, abinda ya kai ga kai shi ‘gobe-da-nisa’ a asibiti an taimaka masa yin numfashi da na’ura, kafin ya samu sauki.

Bayan Johnson, shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, shi ne shugaba na biyu da ya kamu da cutar a watan Afrilu, bayan ya yi ta ikrarin rashin amincewa da cutar, abinda ya kai ga saukar ministocin lafiyar sa guda 3, da kuma mayar da Brazil kasa ta uku na yawan mutanen da suka mutu a duniya sakamakon annobar.

Sai kuma shugaba Juan Orlando Hernandez na Honduras, wanda shi ma aka kwantar a asibiti sakamakon cutar, sai kuma shugaban Belarus Alexander Lukashenko da shugaban Guatemala Alejandro Giammattei.

Sauran sun hada da shugaban Bolivia Luis Abinader da mataimakin shugaban kasar India, M, Venkaiah Naidu.

Ya zuwa yanzu cutar ta hallaka mutane sama da 200,000 a Amurka kasar da ta samu mutane sama da miliyan 6 da suka harbu da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.