Isa ga babban shafi
Covid-19

Matalautan kasashe ne za su amfani da rabin maganin Covid-19 da za a samar -Gavi

Akalla alluran rigakafin cutar Coronavirus miliyan dari daga cikin wadanda za a samar miliyan 200 nan gaba kadan ne za a aike da su kasashe matalauta a shekarar 2021, kamar yadda hadakar kungiyoyin da ke fafutukar samar da daidaito a rigakafin wato Gavi ta sanar.

Zuwa shekarar 2021 hadakar ta Gavi na shirin samar da alluran rigakafin cutar akalla miliyan 200 ko fiye.
Zuwa shekarar 2021 hadakar ta Gavi na shirin samar da alluran rigakafin cutar akalla miliyan 200 ko fiye. Arnd Wiegmann/Reuters
Talla

Wannan mataki ya ninka yawan alluran rigakafin da hadakar kungiyoyin ta Gavi da kuma gidauniyar Bill and Melinda suka sayo daga cibiyar Serum ta India, cibiya mafi girma da ke samar da rigakafi a duniya, biyo bayan yarjejeniyar da suka kula a watan jiya.

Wannan ya kai adadin alluran rigakafin da wannan hadaka ta samar zuwa akalla miliyan 200, a cewar wata sanarwa da Gavi ta fitar a Talatar nan.

Sanarwar ta jaddada cewa yarjejeniyar ta bada zabin samun karin wadannan alluran rigakafi fiye da sau daya har sai sun kai guda miliyan 200 idan akwai bukata, tana mai cewa farashin allura guda zai kai dalar Amurka 3.

A karkashin yarjejeniyar, cibiyar Serum za ta karbi kudi don kara yawan alluran rigkafin da za ta samar, inda kamfanonin AstraZeneca da Novovax za su bunkasa.

Hikimar yin haka ita ce a bai wa kamfanonin yin da alluran rigakafi damar samar da miliyoyin alluran, da zarar an samu amincewar hukumar lafiya ta duniya da hukumar da ke kula da rigakafi.

Shugaban hadakar ta Gavi, Seth Berkley ya karkare a sanarwar da cewa, babu kasar da ya kamata a bar ta a baya a game da rigakafin cutar coronavirus komai talaucinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.