Isa ga babban shafi
Coronavirus

Mutane miliyan 30 sun kamu da Covid-19 a duniya

Adadin mutanen da suka kamu da cutar korona a duniya ya zarce miliyan 30, yayin da dubu 943 da 86 suka rayukansu a daidai lokacin da annobar ke sake dawowa a wasu kasashe.

Coronavirus na barazanar sake barkewa a karo na biyu
Coronavirus na barazanar sake barkewa a karo na biyu indiatimes
Talla

Alkaluman da Hukumar Lafiya ta Duniya ta gabatar sun nuna cewa, yanzu haka mutane miliyan 30 da 62 suka harbu da cutar tun bayan barkewarta a watan Disambar bara, kuma dubu 943 da 86 sun mutu.

Hukumar ta ce, Amurka ke sahun gaba wajen samun wadanda suka kamu da cutar, inda yawansu ya kai miliyan 6 da dubu 650 da 570 kuma dubu 197 da 364 daga cikinsu sun mutu, sai India a matsayi na biyu da mutane miliyan 5 da118 da 253 da suka harbu, kuma dubu  83 da 198 daga cikinsu sun mutu, sannan Brazil a matsayi na 3 da mutane miliyan 4 da 419 da 083 kuma dubu 134 da106 daga cikinsu sun mutu.

Alkaluman hukumar sun ce, nahiyar Asia ke sahun gaba wajen samun wadanda suka harbu a makon jiya, inda yawansu ya kai dubu 742 da 286, sai yankin Kudancin Amurka da Karibiyan mai mutane dubu 493 da 120, sai Turai mai mutane dubu 327 da 524, sannan Amurka da Canada masu mutane dubu  273 da 339.

Gabas ta tsakiya na dauke da mutane dubu 111 da 986, sai Afirka mai mutane dubu 52 da 584 sannan Oceania mai mutane 548.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.