Isa ga babban shafi
Coronavirus

WHO ta nuna damuwa da matakin kasashe na rage kwanakin killace baki

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana damuwa kan matakan da kasashen Turai ke dauka dangane da yakar annobar COVID-19, na rage yawan kwanakin killace bakin da ke zirga-zirga a tsakaninsu.Hukumar ta WHO ta kuma koka kan hadurran da ma’aikatan lafiya ke fuskanta a sassan duniya yayin yakar annobar.

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Yayin wata ganawa da manema labarai a baya bayan nan, babban daraktan hukumar lafiyar ta duniya a Turai Hans Kluge, yace matakan wasu kasashen nahiyar na rage tsawon kwanakin killace mutanen da suka kamu da cutar coronavirus, na tattare hadarin gaske, la’akari da cewar yanzu haka yawan mutanen dake kamuwa da cutar na sake hauhawa bayan saukin da aka samu.

Wasu daga cikin kasasshen da suka rage kwanakin killace marasa lafiyar kuwa sun hada da Birtaniya da Ireland da suka mayar da kwanakin daga 14 zuwa 10, yanzu haka kuma kasashen turai da dama cikinsu harda Croatia da Portugal na nazarin daukar irin wannan mataki, wanda tuni Faransa ta zartas duk da cewa a baya bayan nan sama da mutane dubu 10 suka kamu da cutar ta coronavirus cikin kasar a rana 1.

Kididdigar baya bayan nan da hukumar lafiya ta duniya at fitar, ta nuna cewar, kusan mutane miliyan 5 ne suka kamu da coronavirus a tsakanin kasashen Turai 53, sama da dubu 227 daga cikinsu kuma suka rasa rayukansu a dalilin annobar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.