Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

Coronavirus za ta lakume dimbin rayuka a Oktoba-WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta gargadi cewa, nahiyar Turai za ta fuskanci karuwar mace-mace a lokacin hunturu saboda annobar coronavirus , a dadai lokacin da cutar ta kara kaimi wajen harbar mutane a sassan duniya.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS
Talla

Tuni Isra’ila ta shiga sahun kasashen duniya da ke yaki da sake barkewar annobar coronavirus, inda ta sanar da daukar matakin kulle al’ummarta na tsawon makwanni uku daga ranar Juma’a mai zuwa, tana mai cewa, babu wanda zai yi tafiyar mita 500 daga gidansa.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bada rahoton sabbin mutane dubu 307 da 930 da suka harbu da kwayar cutar a sassan duniya a ranar Lahadi, adadi mafi girma da aka samu tun bayan barkewar annobar a cikin watan Disamban bara a China.

Yanzu haka adadin masu dauke da cutar a sassan duniya ya doshi miliyan 29, yayin da WHO ta ce, cutar za ta tsananta a cikin watannin Oktoba da Nuwamba tare da laukume karin rayuka kamar yadda Hans Kluge, darekta a hukumar ya shaida wa AFP.

Sai dai jami’in ya ce, annobar za ta kawo karshe a lokaci guda.

Tuni mambobi 55 na WHO daga nahiyar Turai suka fara gudanar da taron kwanaki biyu ta kafar intanet domin tattaunawa kan yadda za su tunkari cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.