Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

WHO ta ce ba za ta taba aminta da maganin COVID-19 marar inganci ba

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi ikirarin cewa ko kusa ba za ta taba aminta da wani nau’in magani ko kuma allurar covid-19 da ba ta da cikakken sahihanci ga lafiyar bil’adama, duk da cewa ta damu matuka wajen ganin an wadata duniya da maganin cutar wadda ke ci gaba da kisa.

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO. Christopher Black/WHO
Talla

Shugaban hukumar Tedros Adhanom ya ce duk da yadda gwamnatocin kasashen duniya suka damu matuka wajen ganin an samar da maganin cutar cikin gaggawa ko shakka babu hakan bazai sanya su aminta da amfani da maganin da ke hadari ga lafiya ba.

A cewar shugaban kowanne nau’in maganin cuta na bukatar daukar tsawon lokaci don gudanar masa da gwaje-gwaje gabanin ma fara amfani da shi kan tsirarun mutane kafin daga bisani a sahale amfani da shi baki daya in an aminta da sahihancinsa.

Zuwa yanzu dai kusan mutum miliyan 27 cutar da covid-19 ta kama a sassan duniya baya ga kisan wasu kusan dubu 900.

Kalaman na Tedros Adhanom na zuwa ne dai dai lokacin da Amurka ke shelar fara rarraba na ta nau’in maganin cutar ta covid-19 kwanaki biyu gabanin zaben kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.