Isa ga babban shafi

Zai kai tsakiyar shekarar 2021 kafin wadatuwar maganin coronavirus- WHO

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa babu tabbacin yiwuwar samun wadatuwar maganin annobar COVID-19 kafin nan da tsakiyar shekara mai zuwa, la’akari da cewa kawo yanzu babu masana’antar maganin da ta yi nisa wajen samar da maganin ko kuma allurar.

Kamfanin Pfizer na Amurka ya sanar da cewa samar da nasa nau’in maganin zai kai akalla karshen watan Octoba
Kamfanin Pfizer na Amurka ya sanar da cewa samar da nasa nau’in maganin zai kai akalla karshen watan Octoba Reuters
Talla

Cikin jawabin mai Magana da yawun hukumar Margret Harris ta ce kawo yanzu babu ko da kamfani guda da ya kai nisan kashi 50 cikin dari a gwaje-gwajen samar da maganin cutar ta COVID-19 wanda ke nuna akwai bukatar karin lokaci gabani samu da kuma wadatuwar maganin ko kuma allurar cutar zuwa sassan duniya.

A watan Agusta ne WHO ta amince da baiwa Rasha damar samar da maganin bayan da kasar ta shafe kusan watanni biyu ta na aiwatar da gwajin nau’in maganin na ta kan bil’adama gabanin gabatar da shi ga hukumar ko da ya ke tuni nau’in maganin samfurin Rasha ya gamu da kakkausar suka daga kasashen Turai.

A bangare guda kamfanin Pfizer na Amurka ya sanar da cewa samar da nasa nau’in maganin zai kai akalla karshen watan Octoba, kwanaki kalilan gabanin zaben kasar na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Mai Magana da yawun Hukumar ta WHO Harris yayin taron manema labaran da hukumar ta kira a Geneva, ta ce wadannan dalilai na nuni da cewa zai kai akalla tsakiyar shekara mai kamawa gabanin samun wadatuwar maganin a sassan duniya.

A cewarta WHO da hadin gwiwar GAVI ne za su aikin sanya ido wajen samar da wadatuwar maganin na COVID-19 karkashin shirin COVAX wanda Amurka ta fitar da kanta daga ciki, yayinda kuma za a rika tattara bayanai na kowanne kamfanin ga kasashen da ke goyon bayan shirin fiye da 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.