Isa ga babban shafi
Coronavirus-Afrika

Novavax zai yiwa mutane dubu 3 gwajin maganin COVID-19 a Afrika ta kudu

Katafaren kamfanin harhada magunguna na Novavax da ke Amurka ya sanar da shirin fara rukuni na biyu na gwajin maganin cutar COVID-19 a Afrika ta kudu yau Litinin, gwajin da kamfanin ke cewa za a aiwatar da shi ne kan matasa kusan dubu 3.

Kawo yanzu kasar Afrika ta kudu ita ce ta biyar mafi yawan masu dauke da cutar COVID-19 da jumullar mutum dubu 587 da 653.
Kawo yanzu kasar Afrika ta kudu ita ce ta biyar mafi yawan masu dauke da cutar COVID-19 da jumullar mutum dubu 587 da 653. Reuters
Talla

Kamfanin na Novavax da ke gudanar da wannan gwaji yau Litinin a Afrika ta kudu ya ce gwajin zai gudana ne kan mutane dubu 2 da 665 masu koshin lafiya, sai kuma wasu 240 na daban ciki har da masu HIV.

Sanarwar da kamfanin ya fitar ya ce ya zabi aiwatar da gwajin a Afrika ta kudu ne sakamakon yadda cutar ta COVID-19 ke ci gaba da tsananta, inda ya ke da kwarin gwiwar samun gamsasshen sakamako.

Kawo yanzu kasar Afrika ta kudu ita ce ta biyar mafi yawan masu dauke da cutar COVID-19 da jumullar mutum dubu 587 da 653 ciki kuwa har da mutane dubu 11 da 677 wadanda cutar ta kashe.

A cewar Gregory Glenn jagoran gwajin rukuni na 2 na kamfanin Novavax hatta gidauniyar Bill Melinda ta tallafawa aikin da tsabar kudi dala miliyan 15.

Cikin sanarwar da kamfanin ya fitar, ya ce suna da shirin aiwatar da makamancin rukunin gwajin na 2 a kasashen Amurka da Australia wani lokaci a nan gaba wanda za a aiwatar da shi kan mutane dubu 1 da 500, baya ga fadada gwaje-gwajensa kafin nan da karshen shekara kamar yadda a alkawarta a farkon shekarra nan.

Tun cikin watan Yuli ne gwamnatin Amurka ta baiwa kamfanin na Novavax dala biliyan 1 da miliyan 600 don aiwatar da gwaje-gwajen maganin cutar ta COVID-19 inda ya alkawarta samar da maganin akalla miliyan 100 nan da watan Janairun badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.