Isa ga babban shafi

Coronavirus: Rayuka kusan dubu 5 sun salwanta a sassan duniya cikin sa'o'i 24

Duk da cewa wasu kasashe na bada rahotan raguwar kaifin cutar coronavirus, da alama har yanzu tsugunno bata kare ba, domin kuwa cikin sa’o’i 24 da suka gabata kadai, mutane kusan dubu 5 annobar ta halaka a fadin duniya, wasu dubu 106 kuma suka kamu da cutar.

Masu aikin hakon kabari a Vila Formosa dake Sao Paulo, makabarta mafi girma a Brazil, yayin rufe gawar wani da annobar coronavirus ta kashe. 13/5/2020.
Masu aikin hakon kabari a Vila Formosa dake Sao Paulo, makabarta mafi girma a Brazil, yayin rufe gawar wani da annobar coronavirus ta kashe. 13/5/2020. REUTERS/Amanda Perobelli
Talla

A halin da ake ciki yawan wadanda suka kamu da wannan cuta ta coronavirus a kasashe da manyan yankuna 196, ya kai miliyan 5 da dubu 49 da 390, daga cikinsu kuma dubu 329 da 799 sun mutu, yayinda akalla miliyan 1 da dubu 867 da 800 suka warke.

Sabbin alkalumma dai na nuni da cewar kaifin annobar ta coronavirus ya karkata zuwa nahiyar Kudancin Amurka, la’akari da hauhawar adadin mutanen da cutar ke halaka da wadanda suke kamuwa da ita, inda Brazil ke kan gaba.

Sai dai har yanzu annobar tafi tafka barna a Amurka inda ta halaka mutane dubu 93 da 863, sai Birtaniya mai mutane dubu 36 da 42, yayinda a Italiya cutar ta halaka mutane dubu 32 da 486.

Faransa mutane dubu 28 da 215 ta rasa, Spain kuma dubu 27 da 940.

Brazil kasar da annobar ta fi halakawa jama’a a yankin Latin, zuwa yanzu mutane dubu 20 da 47 cutar ta kashe mata, daga cikin jumillar mutane akalla dubu 310 da suka kamu, abinda ya sanya ta zama kasa ta uku a duniya wajen yawan masu dauke da cutar bayan Amurka da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.