Isa ga babban shafi
Duniya-Coronavirus

Rayukan da coronavirus ta lakume a kasashe 196 sun haura dubu 325

Sama da mutane dubu 325 annobar coronavirus ta halaka a fadin duniya zuwa safiyar yau, kuma alklumman hukumomin lafiya sun nuna cewar, nahiyar Turai da Amurka, ke da kashi 3 bisa 4 na adadin mamatan.

Asibitin Gilberto Novaes dake Manaus a kasar Brazil.
Asibitin Gilberto Novaes dake Manaus a kasar Brazil. AFP / MICHAEL DANTAS
Talla

Sabuwar kididdigar da hukumomin lafiya suka fitar ta ce cikin sa’o’i 24 da suka gabata kadai, mutane dubu 4 da 951 annobar coronavirus ta kashe, yayinda karin wasu dubu 94 da 820 suka kamu da cutar.

Sabon adadin ya sanya jumillar yawan mutanen da cutar ta kashe a tsakanin kasashe 196 kaiwa dubu 325 da 232, daga cikin mutane miliyan 4 da dubu 943 da 50 da suka kamu da cutar, wadanda kuma akalla miliyan 1 da dubu 827 da 200 suka warke.

Kasashen da wannan annoba ta fi yiwa barna a duniya sun hada da Amurka, inda a nan kadai rayukan mutane dubu 92 da 583 coronavirus ta lakume, biye kuma Birtaniya ce, bayan rasa mutane dubu 35 da 704, yayinda a Italiya cutar da halaka dubu 32 da 330.

Faransa ta rasa mutane dubu 28 da 132, sai Spain mai mutane dubu 27 da 888.

A Afrika kuma jumillar mutane dubu 2 da 973 coronavirus ta halaka, daga cikin dubu 93 da 772 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.