Isa ga babban shafi
Duniya

Coronavirus ta salwantar da rayukan sama da mutane dubu 315

Hukumar Lafiya ta duniya tace adadin mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a fadin duniya sun haura dubu 315, yayinda yawan wadanda suka kamu da cutar a yanzu ya haura miliyan 4 da dubu 700, a jumillar kasashe 196.

Wasu masu fama da cutar coronavirus a asibitin Circolo dake garin Varese a Italiya. 1/4/2020.
Wasu masu fama da cutar coronavirus a asibitin Circolo dake garin Varese a Italiya. 1/4/2020. REUTERS/Flavio Lo Scalzo
Talla

Sabbin alkalumman na yau dai sun nuna cewar, tun bayan bullarta daga China a watan Disambar bara, annobar coronavirus ta halaka jumillar mutane dubu 315 da 270, daga cikin miliyan 4 da dubu 727 da 220 da ta kama a fadin duniya.

Kawo yanzu kuma akalla mutane miliyan 1 da dubu 700 sun warke daga cutar.

Annobar ta fi tafka barna a Amurka bayan halaka mutane dubu dubu 89 da 564 a kasar, sai Birtaniya a matsayi na biyu bayan rasa mutane dubu 34,636, sai Italiya mai mutane 31,908, a Faransa jumillar mutane dubu 28 da 108 annobar ta halaka, a Spain kuma ta kashe dubu 27 da 659.

Nahiyar Latin ta rasa mutane dubu 29 da 493, sai Asiya mai mutane dubu 12 da 394, Gabas ta Tsakiya kuma dubu 8 da 204, yayinda Afrika ta rasa mutane dubu 2 da 765.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.