Isa ga babban shafi
Coronavirus-Duniya

Coronavirus ta halaka mutum 4,981 a kwana 1, dubu 96 kuma sun kamu

Hukumar Lafiya ta duniya tace adadin mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a fadin duniya sun kai 304,619, yayinda cutar ta kama mutane kusan miliyan 4 da rabi, kana miliyan guda da rabi sun warke.

Wasu manyan kaburbura da ake binne wadanda annobar coronavirus ta halaka a birnin New York. 9/4/2020.
Wasu manyan kaburbura da ake binne wadanda annobar coronavirus ta halaka a birnin New York. 9/4/2020. REUTERS/Lucas Jackson
Talla

Alkalumman hukumar sun nuna a cikin sa’oi 24 da suka gabata, mutane 4,981 suka mutu kuma 1,759 sun fito ne daga Brazil, yayinda aka samu sabbin wadanda suka harbu da cutar 96,039 a fadin duniya.

Har yanzu Amurka ke sahun gaba da mamata 86,744, sai Birtaniya a matsayi na biyu da mutane 33,998, sai Italiya mai mutane 31,610, sai Faransa mai mutane 27,529, yayinda Spain ke da mutane 27,459.

Daga cikin jumillar mutane 304,619 da annobar ta coronavirus ko COVID-19 ta kashe, 164,137 sun fito ne daga nahiyar Turai, sai Amurka da Canada mai mutane 92,386 sannan Afirka mai mutane 2,601.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.